Bangaren kasa da kasa, gagarumar nasarar da kungiyar ikhwanul muslimin ta samu a zaben da aka gudanar a kasar Masar na tabbatar da cewa hramtacciyar kasar Isra’ila na cikin wani yanayi na damuwa matuka wanda hakan zai haifar dawani gagarumin juyi a cikin alakarta da kasar Masar.
A zanatawar da ta hada kamfanin dilalncin labaran iqna da wani masani kan harkokin kasar Ethiopia kuma kuma sani kan lamurran nahiyar Afirka Zuga Ayata ya bayyana cewa, nasarar da kungiyar ikhwanul muslimin ta samu a zaben da aka gudanar a kasar Masar na tabbatar da cewa hramtacciyar kasar Isra’ila na cikin wani yanayi na damuwa matuka wanda hakan zai haifar dawani gagarumin juyi a cikin alakarta da kasar Masar wadda ita ce babbar kasar larabawa da take da alaka da ita ta diplomasiyya da harkokin soji.
Kungiyar ‘yan uwa musulmi dai ta samu gagarumin rinjaye a mafi yawan kuriun da aka kada na zaben ‘yan majlaisar dokokin kasar Masar, lamarin da ke tabbatar da cewa abubuwan da suke faruwa na mikewar al’ummomin larabawa yan ada dangataka da musulunci, domin kuwa wadanda suke bayyana muslunci cikin manufofinsu ne suke samun nasara.
Nasarar da kungiyar ikhwanul muslimin ta samu a zaben da aka gudanar a kasar Masar na tabbatar da cewa hramtacciyar kasar Isra’ila na cikin wani yanayi na damuwa matuka wanda hakan zai haifar dawani gagarumin juyi a cikin alakarta da kasar Masar kamar yadda masanin harkokin Afirka ya fada. 911463