IQNA

Jam’iyar Da ‘Yauwa Musulmi Suka kafa A Masar Ce Ta Samu Nasara A Zabe

16:56 - December 08, 2011
Lambar Labari: 2235214
Bangaren kasa da kasa, sakamakon karshe da aka fitar na zaben ‘yan majalisar dokokin kasr bangare na biyu na tabbatar da cewa ya zuwa yanzu dai jamiyar adalci da ‘yanci da kungiyar ‘yan uwa musulmi ta kafa ce ta lashe akasarin kujerun majalisar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton da ya nakalto daga tashar talabijin din Al-alam an bayyana cewa, sakamakon karshe da aka fitar na zaben ‘yan majalisar dokokin kasr bangare na biyu na tabbatar da cewa ya zuwa yanzu dai jamiyar adalci da ‘yanci da kungiyar ‘yan uwa musulmi ta kafa ce ta lashe akasarin kujerun majalisar kasar.
Wasu masana dai sun amanar cewa nasarar da kungiyar ikhwanul muslimin ta samu a zaben da aka gudanar a kasar Masar na tabbatar da cewa hramtacciyar kasar Isra’ila na cikin wani yanayi na damuwa matuka wanda hakan zai haifar dawani gagarumin juyi a cikin alakarta da kasar Masar wadda ita ce babbar kasar larabawa da take da alaka da ita ta diplomasiyya da ma wasu harkokin na daban.
Jam’iyar ‘yan uwa musulmi dai ta samu gagarumin rinjaye a mafi yawan kuriun da aka kada na zaben ‘yan majlaisar dokokin Masar, lamarin da ke tabbatar da cewa abubuwan da suke faruwa na mikewar al’ummomin larabawa yan ada dangataka da musulunci, domin kuwa wadanda suke bayyana muslunci cikin manufofinsu ne suke samun nasara a dukkanin kasashen da aka juyi, misali Tunisia da kuma masar yanzu.
Wannan nasarar da kungiyar ikhwanul muslimin ta samu a zaben da aka gudanar a kasar Masar na tabbatar da cewa hramtacciyar kasar Isra’ila na cikin wani yanayi na damuwa matuka wanda hakan zai haifar da wani gagarumin juyi a cikin alakarta da kasar.
911423





captcha