Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga sabbin shiga muslunci a kasar Birtnaiya kan ilmomin kur’ani da kuma sauran ilmomin shari’ar musulunci da suka hada da hukunce-hukuncen addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na ic-el cewa, ana shirin fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga sabbin shiga muslunci a kasar Birtnaiya kan ilmomin kur’ani da kuma sauran ilmomin shari’ar musulunci da suka hada da hukunce-hukuncen addini da sauran abubuwan da ya kamata su sani, wanda bababr cibiyar kula da harkokin musulunci ta birnin London ta dauki nauyin shiryawa da gudanrwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shirin na daga cikin muhimman ayyukan da wannan cibiya ta saba gudanarwa, domin amfanar da mutanen da suka karbi addinin muslunci a kasar Birtaniya, ko kuma daga wasu kasashe amma suna zaune a kasar.
Yanzu haka dai ana shirin fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga sabbin shiga muslunci a kasar Birtnaiya kan ilmomin kur’ani da kuma sauran ilmomin shari’ar musulunci da suka hada da fikihun addini da kuma wasu muhimman abubuwa da suka danganci makomarsu.
912804