Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na On Islam cewa, mabiya addinin musulunci a kasar Amurka musamman ma likitoci daga cikinsu suna gudanar da wasu ayyuka na jin kai a asibitocin kasar domin taimaka ma mutane marassa lafiya.
Dag acikin likitocin da suke gudanar da irin wannan gagarumin aiki na jin kai har da wata likita mai suna Rasham Khan da take zaune a kasar Amurka, wadda ta kware kan harkokin mata, wadda ta kan je asibitin birnin Mount Plesant domin yin magani ga marassa lafiya kyauta.
Rahoton ya ce mabiya addinin musulunci a kasar Amurka musamman ma likitoci daga cikinsu suna gudanar da wasu ayyuka na jin kai a asibitocin kasar domin taimaka ma mutane da suke kwance a asibitoci suna jinya.
Bugu da kari kan hakan likitoci musulmi suna gudanar da wasu ayyukan a wani asibitin da suka bude, da nufin yin sauki ga musulmi da suke fama da matsaloli na rashin lafiya a kasar.
912672