IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Na Hankoron Hana Yin Kiran Salla A Masallatai

20:02 - December 11, 2011
Lambar Labari: 2236880
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta kudiri aniyar hana yin kiran salla a cikin masallatai da suke yankunan gabar yamma da kogin Jordan domin takura ma musulmi palastinawa wajen hana su gudanar da harkokin addininsu yadda ya kamata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na ajib cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta kudiri aniyar hana yin kiran salla a cikin masallatai da suke yankunan gabar yamma da kogin Jordan domin takura ma musulmi palastinawa wajen hana su gudanar da harkokin addininsu yadda ya kamata a cikin yankunan da yahudawan sahyuniya suka mamaye.
Bayyanin ya ci gaba da cewa shugaban majalisar dokokin yahudawan sahyuniya an mika masa wani daftarin kudiri, wanda yake dauke da kira ga majalisar da ta amince da shi da nufin han ayin kiran salla a cikin yankunan palastinawa, domin kuwa acewarsa wanada suka gabatar da daftarin kudirin sun ce ana takura ma yahudawa da kiran salla.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kudiri aniyar hana yin kiran salla a cikin masallatai da suke yankunan gabar yamma da kogin Jordan domin takura ma musulmi palastinawa wajen hana su gudanar da harkokin addininsu yadda ya kamata a cikin yankunan gabar yamma da koin Jordan da ma saun yankunan da suke kusa da matsugunnan yahudawa.
912614

captcha