IQNA

Tawagar Kungiyar Kasashen Musulmi Za Ta Yi Tafiya Zuwa Kasar Libya

20:01 - December 11, 2011
Lambar Labari: 2236881
Bangaren kasa da kasa, wata tagawa daga kungiyar kasashen musulmi za ta yi tattaki zuwa kasar Libya domin ganawa da sabbin jami’an kasar kan lamurra da suka danganci irin gudunmawar da kungiyar za ta iya bayarwa domin habbaka lamurra a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, wata tagawa daga kungiyar kasashen musulmi za ta yi tattaki zuwa kasar Libya domin ganawa da sabbin jami’an kasar kan lamurra da suka danganci irin gudunmawar da kungiyar za ta iya bayarwa domin habbaka lamurra tsakanin bangarorin biyu, bayan kawar da tsohon jagoran kasar ta Libya.
Tun bayan da ‘yan tawaye da suke dauke da makamai, wadanda kasashen yammacin turai suke taimaka musu suka kawar da tsohon jagoran Libya mu’ammar Gaddafi, kasar take ta fuskantar matsaloli daban-daban, musamman tsakanin jami’an da kuma’yan tawaye da suke dauke da makamai, wadanda suka sha alw2ashinj cewa ba za su taba jiye makamansu ba.
Yanzu haka dai wata tagawa daga kungiyar kasashen musulmi za ta yi tattaki zuwa kasar Libya domin ganawa da sabbin jami’an kasar kan lamurra da suka danganci irin gudunmawar da kungiyar za ta iya bayarwa domin habbaka lamurra da suka danganci rayuwar fararen hula.
912487


captcha