Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Akmaluddini Aiglo zai nufi kasar Libya domin ganawa da shugaban majalisarwucin gadi ta kasar Mustafa Abduljalil a birnin Tripoli fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na oic-oci web cewa babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Akmaluddini Aiglo zai nufi kasar Libya domin ganawa da shugaban majalisarwucin gadi ta kasar Mustafa Abduljalil a birnin Tripoli fadar mulkin kasar kamar dai yadda majiyoyin kungiyar suka bayyana.
Shugaban kungiyar zai tattauna muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu, musamman habbaka dangataka da kuma sani bangarorin da za a taimaka ma kasar Libya wadda a halin yanzu take cikin yanayi na murmurewa, bayan kaddamar da yaki kan kasar da kasashen yammacin turai suka yi kan kasar.
Babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Akmaluddini Aiglo zai nufi kasar Libya domin ganawa da shugaban majalisarwucin gadi ta kasar Mustafa Abduljalil a birnin Tripoli fadar mulkin kasar wanda ya yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shiryen wannan ziyara.
915844