Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wakilan majalisar datijja a kasar Holland sun bayyana cewa daftarin shawara da jam'iyar kare hakkin dabbobi ta gabatar na hana yanka dabbobi yanka na halaliya bai samu karbuwa ba domin yawancin yan majalisar sun jefa kuri'ar watsi da shi.A watan Tir na wannan shekara ne jam'iyar da ke raya kare hakkin dabbobi a kasar ta Holland ta shigar da wannan shawara ta hanay yanka dabbobi karkashin tsarin yanka na addinin musulunci kuma bayan bincike da tabka mahawara a majalisar yawancin yan majalisar datijjan kasar suka jefa kuri'ar watsi da wannan shawara ta samara da dokara hana yanka dabbobin karkashin tsarin addinin musulunci .Lamarin da ake kollonsa a matsayin babbar nasara ga musulmin wannan kasar da kuma sauran musulmi na duniya .
916524