IQNA

Ficewar Amurka Daga Iraki Ya Tabbatar Da Karfin Gwagwarmayar Irakawa

14:48 - December 21, 2011
Lambar Labari: 2242929
Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa ficewar da sojojin mamayar Amurka suka yi daga kasar Iraki ya tabbatar da karfi da kuma tsayin daka da masu fatattakar ‘yan mamaya a kasar.
Kamafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar cewa, Sayyid Hashim Safiyuddin shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa ficewar da sojojin mamayar Amurka suka yi daga kasar Iraki ya tabbatar da karfi da kuma tsayin daka da masu fatattakar ‘yan mamaya a kasar ta Iraki, musamman ma awannan lokaci da Amurka take cikin rudu.
Ya ci gaba da cewa masu tunanin za su iya rusa gwagwarmayar musulunci suna tunain ne maras tushe, domin kuwa jihadi da ake saboda Allah ba shi da wata danganta da rudu na abin duniya ko rayu da kyele-kyalenta, masu jihadi kullum suna shaukin samun shahda ne a tafarkin Allah, kuma wani abu ba ya tsoratar da su.
Sayyid Safiyuddin shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa ficewar da sojojin mamayar Amurka suka yi daga kasar Iraki ya tabbatar da karfi da kuma tsayin daka da masu fatattakar ‘yan mamaya a kasar wadda ta sha gwagwarmaya tsawon shekaru.
919485

captcha