Bangaren kasa da kasa: Munsaf Marzuki shugaban jamhuriyar Tunusiya a ranar ashirin da takwas ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya yi wata ganawa ta musamman da shugabannin mazhabobin adinin musulunci ,addinin kirista da kuma addinin yahudanci inda suka tattauan da shi kan lamura da suka shafi kasar ta tunusiya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : Munsaf Marzuki shugaban jamhuriyar Tunusiya a ranar ashirin da takwas ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya yi wata ganawa ta musamman da shugabannin mazhabobin adinin musulunci ,addinin kirista da kuma addinin yahudanci inda suka tattauan da shi kan lamura da suka shafi kasar ta tunusiya.Daga cikin adanda suka halarci wannan ganawa akwai Shekh Usman Batikh babban muffin kasar Tunusiya da Haitaim Baitan jagoran yahudawan kasar da kuma Marum Laham inda suka tattauna matsalolin da ke addabar wannan kasa ta fuskar addini da zamantakewa da kuma tunanin hanyoyin magance irin wadannan matsaloli domin ciyar da kasar da kuma sake gina tat a bangarori da suka hada da addini da siyasa da tattalin arziki da kuma ilimi da duk wani bangare day a shafi zamantakewar kasar.
919118