Bangaren kasa da kasa: komitin musulmin kasar Faransa a ranar daya ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya fitar da wani bayani da a cikinsa ke nuna damuwa matuka gaya da Karin yawaitar kai hare haren nuna wariya kan masallatai da guraren da cibiyoyin Ibadar musulmi a wannan kasa ta Faransa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; komitin musulmin kasar Faransa a ranar daya ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya fitar da wani bayani da a cikinsa ke nuna damuwa matuka gaya da Karin yawaitar kai hare haren nuna wariya kan masallatai da guraren da cibiyoyin Ibadar musulmi a wannan kasa ta Faransa.Safir Niyoz jagoran komitin musulmin kasar ta Faransa dangane da wannan labarin ya bayyana cewa; a cikin watannin biyu da suka gabata kawai masu nuna tsananin adawa kan musulmi da nuna wariya da banbanci kan musulmi sun kai wa akalla masalatai shida a fadin kasar hari da haka ke nuna da lamari mai muni da tabarrarewa tsaro da zamantakewar al'ummar Faransa kuma wadannan hare haren nuna wariya da aka kai wa masallatai da guraren ibadar musulmi a biranai daban daban na kasar ta faransa an kai sun e a cikin watannin biyu da suka gabata zuwa ranar ashirin da watan desamba da muke ciki.
920795