IQNA

Hizbullahi Ta Yi Allah wadai da Harin Bom Na Ta'addanci A Bagadaza

13:15 - December 24, 2011
Lambar Labari: 2244083
Bangaren kasa da kasa: bangaren gwagwarmaya a kungiyar musulunci ta Labanon wato kungiyar Hizbullahi a daren daya ga watan dai na wannan shekara ce ta fitar da wani bayani da a ciki take yin Allah wadai da tofin Allah tsine kan jerin hare-haren ta'addanci a birnin Bagadaza fadar mulkinkasar Iraki.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; bangaren gwagwarmaya a kungiyar musulunci ta Labanon wato kungiyar Hizbullahi a daren daya ga watan dai na wannan shekara ce ta fitar da wani bayani da a ciki take yin Allah wadai da tofin Allah tsine kan jerin hare-haren ta'addanci a birnin Bagadaza fadar mulkinkasar Iraki.Kamar yadda jaridar Al'intikad da ke fito a kasar Labanon a cikin wannan bayani kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a labanon ta ce Amerika nada hannu a cikin fashe fashen bamabaman .A wannan hari na safiyar ranar alhamis a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki yayi sanadiyar mutuwar mutane da daman gaske balantana wadanda suka jikkata kuma a kai hare haren fashewar bama bamai da dama lamarin da ke nemnan ya maido da tabarbarewar sha'anin tsaro da kai hare haren ta'aaddanci ta hanyar fasa bama-bamai.

920781

captcha