IQNA

Kungiyar Hizbullah A Kasar Lebanon Ta Yi Allawadai Da Harin Birnin Damascus

19:22 - December 25, 2011
Lambar Labari: 2245017
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Lebanon ta yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai akasar Syria wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da hamsin da jikkatar wasu sama da dari daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almanar cewa, Hizbullah a kasar Lebanon ta yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai akasar Syria wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da hamsin da jikkatar wasu sama da 100 a ranar Juma'a da ta gabata.

A nata bangaren jamhuriyar muslunci ta Iran ta yi kakkausar suka kan harin ta'addancin da aka kai jiya a kasar Syria, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla hamsin tare da jikkar wasu sama da dari daya.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai yau a birnin Tehran, kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Ramin Mehman Parast ya bayyana cewa, makiya al'ummar Syria suna hankoron ganin sun daidaita kasar ta hanyar taimaka ma 'yan ta'adda da suke aikata irin wannan ta'asa, kuma babbar manufar hakan ita ce kawo barazana ga zaman lafiya a kasashen yankin gabas ta tsakiya baki daya.

A nata bangaren gwamnatin kasar Syria ta dora alhakin kai harin ta'addancin a kan kungiyar alka'ida, bisa bayanan da ta samu da ke tabbatar da cewa daruruwan 'yan alkaida daga kasashen larabawa sun shiga cikin kasar da sunan cewa masu adawa ne da gwamnatin kasar Syria.

921078

captcha