Bangaren kasa da kasa, Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya Faisal Miqdad ya bayyana cewa; Wadannan hare-haren ta'addanci suna kara tabbatar da da'awar gwamnatin Siriya ce da ke bayyana cewa; wasu gungun 'yan ta'adda ne da suke amfani da makamai domin ganin bayan gwamnatin Siriya ke tada kayan baya a kasar, kuma suna aiwatar da kisan gilla kan jami'an tsaron kasar da fararen hula
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin din gwamnatin kasar ta Siriya "Sana" ta fayyace cewa: A safiyar jiya juma'a ce aka kai hare-haren ta'addanci kan babbar cibiyar ma'aikatar leken asirin Siriya da wata karamar cibiyar tsaron kasar da suke birnin Damaskas fadar mulkin kasar, inda hare-haren ta'addancin suka yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 50 tare da jikkata wasu fiye da 100 na daban, kuma mafi yawan mutanen da hare-haren ta'addancin suka ritsa da su fararen hula ne. Kamar yadda hare-haren suka janyo hasarar dukiyoyi tare da lalata gine-gine da suke yankunan da aka kai hare-haren.
Jami'an gwamnatin kasar Siriya sun bayyana cewa: Bincike ya tabbatar da hannun 'yan kungiyar Al-Qa'ida a shirya kai hare-haren biyu tare da aiwatar da su, kuma wasu rahotannin suna nuni da cewa; tuni jami'an tsaron kasar ta Siriya suka sami nasarar kama wasu mutane biyu da suke zargi da hannu a kai hare-haren.
An kai hare-haren ta'addancin ne kwana daya kacal bayan isar tawagar farko ta wakilan kungiyar hadin kan kasashen larabawa da zasu sanya ido kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Siriya da kungiyar ta Larabawa kan hanyar shawo kan rikicin da ya kunno kai a kasar ta Siriya tun a watan Maris na wannan shekara.
922080