IQNA

Kungiyar Hamas Ta Yi Gargadi Kan Yunkurin Yahudantar Da Qods

16:53 - December 27, 2011
Lambar Labari: 2246477
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi kan hankoron da yahudawan sahyuniya suke yi na yahudantar da birnin Qods mai alfarma da nufin mayar da palastinawa saniyar ware.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dil Almanar cewa, kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi kan hankoron da yahudawan sahyuniya suke yi na yahudantar da birnin Qods mai alfarma da nufin mayar da palastinawa saniyar ware acikin dukaknin harkokin yankin.
Bayanin na kungiyar Hamas ya ce babban abin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke nufi da wannan mataki shi ne mamaye sauran yankunan palastinawa da suke gabacin birnin Qods mai alfama, tare da share duk wasu sauaran alamu na tarihin musulunci da addinin kirista da ke cikin wannan birnin Mai albarka.
A cikin bayanin da kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta fitar ta yi gargadi kan hankoron da yahudawan sahyuniya suke yi na yahudantar da birnin Qods mai alfarma da nufin mayar da palastinawa saniyar ware a yankin baki daya.
A jiya ne majalisar kenest ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta gudanar da zam, inda ta amince da birnin Qods a matsayin babbar birnin kasar Yuhudsawan sahyuniya.
922997


captcha