Bangaren kasa da kasa, tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak zai sake bayyana a gaban kotun kasar domin fuskakantar shari’a kan laifuka da ya aikata kan masu bore da suka yi sanadiyar hambare gwamnatinsa.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad ta kasar Lebanon cewa, yan haka dai tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak zai sake bayyana a gaban kotun kasar domin fuskakantar shari’a kan laifuka da ya aikata kan masu bore da suka yi sanadiyar hambare gwamnatinsa tare mukarrabansa.
Bayanin ya ce za a gudanar da wannan shari’a ne a ranar gobe Laraba tare da halartar Mubarak a cikin keji da sauran mutane shida , da suka hada ‘ya’yansa biyu Jamal Mubarak da Ala gami da Habib Aladli tsohon ministan harkokin cikin gidan kasar Masar, wanda ake zargi da hannu wajen bayar da umurni kan kisan masu zanga-zanga.
Rahotanni sun ce tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak zai sake bayyana a gaban kotun kasar domin fuskakantar shari’a kan laifuka da ya aikata kan masu bore da suka yi sanadiyar hambare gwamnatinsa wadda ta yi bakin mulki a kan al’ummar kasar Masar, tare da kare manufofin yahudawan sahyuniya.
922891