Bangaren kasa da kasa, babban kwamitin hadin gwiwa na musulmi da kiristoci a yankin palastinu ya yi kakkausar da yin Allawadai da yunkurin haramtacciyar kasar Isra’ila na mayar da birnin Qods mai alfarma fadar mulkinta.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Info cewa, babban kwamitin hadin gwiwa na musulmi da kiristoci a yankin palastinu ya yi kakkausar da yin Allawadai da yunkurin haramtacciyar kasar Isra’ila na mayar da birnin Qods mai alfarma fadar mulkintabayan gabatar da daftarin doka kan hakan a gaban majalisar Keneset.
A nata bangaren kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi kan hankoron da yahudawan sahyuniya suke yi na yahudantar da birnin Qods mai alfarma da nufin mayar da palastinawa saniyar ware a cikin dukaknin harkokin yankin, da kuma mamaye kasarsu.
Yanzu haka dai babban kwamitin hadin gwiwa na musulmi da kiristoci a yankin palastinu ya yi kakkausar da yin Allawadai da yunkurin haramtacciyar kasar Isra’ila na mayar da birnin Qods mai alfarma fadar mulkinta, tare da kiran dukaknin mulmi da kiristoci da sauran mutanen duniya masu lamiri, da su taka wa wannan makrci birki.
922792