IQNA

Kuwait Za Ta Girmama Wadanda Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur'ani

21:33 - December 28, 2011
Lambar Labari: 2247357
Bangaren kasa da kasa, Kuwait za ta girmama wasu daga cikin wadanda suka halarci gasar karatun kur'ani mai tsarki kuma suna kwazo a bangaren harda da kuma tajwidi, sai kuma bangaren tilawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alanba cewa, gwamnatin kasar Kuwait za ta girmama wasu daga cikin wadanda suka halarci gasar karatun kur'ani mai tsarki kuma suna kwazo a bangaren harda da kuma tajwidi, sai kuma bangaren tilawa da hakan ya hada da bangaren tartili da kuma tangim.

Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Kuwait din ce ta dauki nauyin shirya gasar, tare da daukar nauyin dukaknin abubuwan da za a bayar na daga kyautuka ga wadanda suka nuna kwazon, kamar dai yadda kakakin ma'aikatar ya sanar a jiya, haka nan kuma taron zai samu halartar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin.

Kuwait za ta girmama wasu daga cikin wadanda suka halarci gasar karatun kur'ani mai tsarki kuma suna kwazo a bangaren harda da kuma tajwidi, sai kuma bangaren tilawa kamar dai yadda aka sanar.

Babbar cibiya kula da harkokin karatu da shirya gasar kur'ani mai tsarki a kasar ce ke kan gaba wajen shirya irin wadannan taruka a kasar Kuwait.

923625


captcha