Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Taron kasa da kasa kan Irfani da Sufiya da mazhabar Maridiya ta shirya a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.Wannan taro an gudanar da shi daga ranar biyu ga watan dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku d atis'in hijira shamsiya zuwa biyar ga watan inda wakilai daga kasashe da dama kun da wakilan mazhabobi daban daban na addini daga kasashen suka hadu a birnin na Dakar na kasar Senegal domin tattauna wadannan mahangogi biyu na Irfani da sufiya .Shugaban kasar Senegal Abdalla Wade ne ya gabatar da taron bude wannan taro inda ya yi bayanbi kan muhimmancin Irfani da sufiya da irin koyarwa da ke tattare da wadannan mahangogi guda biyu ta fuskar ma'anawiya da muhimmancin sanin wadannan abubuwa biyu.
924797