IQNA

Mutanen Masar Ba Su Amince Da Sallamar Wadanda Ake Zargi Da Kisan Masu Bore Ba

15:21 - December 31, 2011
Lambar Labari: 2248541
Bnagaren kasa da kasa, dubban mutane a yankin sayyidah Zainab da ke cikin birnin Alkahira na kasar Masar sun yi cincirindo kan titunan yankin domin nuna rashin amincewa da hukuncin da kotun kasar ta yanke na sallamar mutaen da suke da hannu a kisan da aka yi wa masu bore.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, dubban mutane a yankin sayyidah Zainab da ke cikin birnin Alkahira na kasar Masar sun yi cincirindo kan titunan yankin domin nuna rashin amincewa da hukuncin da kotun kasar ta yanke na sallamar mutaen da suke da hannu a kisan da aka yi wa masu boren da aka yi a kasar wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na Husni Mubarak.
Wadanda suka yi zanga-zangar sun yi ta rera taken kalmar shahada tare da nemana yi hukunci na gaskiya da adalci kan mutanen mubarak da suka kashe mutane a lokacin juyin juya halin kasar, domin kuwa mutaen dukkansu ana zargin da hannu dumu-dumu a wannan tabargaza da ta afku a kasar.
Mutane a yankin sayyidah Zainab da ke cikin birnin Alkahira na kasar Masar sun yi cincirindo kan titunan yankin domin nuna rashin amincewa da hukuncin da kotun kasar ta yanke na sallamar mutaen da suke da hannu a kisan da aka yi wa masu boren da aka yi a kasar wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na Husni Mubarak a farkon shekarar da ta gabata.
925535
captcha