IQNA

Wani Bam Ya Tarwatse A Cikin Wata Makarantar Kur’ani A Nigeria

15:22 - December 31, 2011
Lambar Labari: 2248543
Bangaren kasa da kasa, wani bam da aka dana acikin wata makarantar kur’ani a yankin Niger Delta da ke kudancin tarayyar Nigeria ya tarwatse kuma ya yi sanadiyyar jkikkatar wasu daga cikin daliban makarantar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na AllAfrica cewa, a ranar laraba da ta gaba ne wani bam da aka dana acikin wata makarantar kur’ani a yankin Niger Delta da ke kudancin tarayyar Nigeria ya tarwatse kuma ya yi sanadiyyar jkikkatar wasu daga cikin daliban makarantar a wani mataki da ake ganin ya yi kam ada na daukar fansa kan mabiya addinin muslunci da suke zaune a wannan yanki, wanda akasarin mazaunansa mabiya addinin kirista ne.
Rahoton bayan kai harin a nan take dai yara bakwai ne daga cikin masu karatun kur’ani wannan makaranta suka samu raunuka, kuma a nan take a ka dauke su zuwa asibiti domin yi musu maganai, haka nan kuma makonni biyu kafin wannan lokacin ma wani bam din ya tashi a cikin wani masallaci da ke yankin, wanda shi ma ya yi sanadiyar lalacewar wasu ababuwan masallacin.
Bam din da aka dana a cikin makarantar kur’anin a yankin Niger Delta da ke kudancin tarayyar Nigeria wata manuniya ce ta rashin tsaro a Nigeria, kuma hakan yana yin ishara da cewa akwai rikici a kasar matukar dai mahukunta ba su dauki matakan da suka dace ba.
925529

captcha