Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatun kur’ani mai tsarki dta kasa baki daya a kasar Sin, wadda aka gudanar a birnin Beijin fadar mulkin kasar tare da halartar makaranta kur’ani mai tsarki daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na arabic1people.com, an kawo karshen gasar karatun kur’ani mai tsarki dta kasa baki daya a kasar Sin, wadda aka gudanar a birnin Beijin fadar mulkin kasar tare da halartar makaranta kur’ani mai tsarki daga sassa daban-daban na kasar ta China.
Kimanin makaranta sittin 60 ne daga sassa na lardunan kasar suka halarci wannan gasa daga larduna 23, kuma gasar ta samu karbuwa da armashi kamar yadda wasu da suka halarci wannan gasa suka bayyana.
A jiya ne aka kawo karshen gasar karatun kur’ani mai tsarki dta kasa baki daya a kasar Sin, wadda aka gudanar a birnin Beijin fadar mulkin kasar tare da halartar makaranta kur’ani mai tsarki daga sassa daban-daban.
Kasar China dai na daga cikin kasashe masu yawan muslmi a duniya, duk kuwa da cewa su ne marassa rinjaye idan aka kwatanta su da sauran mutanen kasar da suke bin wasu addinai na daban.
925497