IQNA

Gwagwarmayar Ce Kawai Hanyar ‘Yantar Da Yankunan Palastawa Da Aka Mamaye

20:24 - December 31, 2011
Lambar Labari: 2248638
Bangaren kasa da kasa, kwamitin kula da harkokin gwagwarmayar palastinaw ad akuma ba ta kariya ya fitar da wani bayani da acikinsa yake jadda cewa gwagwarmaya ce kawai hanyar ‘yantar da dukkanin yankunan palastinawa da haramtcciyar kasar Isra’ila ta mamaye.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewaya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, kwamitin kula da harkokin gwagwarmayar palastinaw ad akuma ba ta kariya ya fitar da wani bayani da acikinsa yake jadda cewa gwagwarmaya ce kawai hanyar ‘yantar da dukkanin yankunan palastinawa da haramtcciyar kasar Isra’ila ta mamaye tun cikin shekara ta 1948 miladiyya.
Kwamitin palastinawa sun bayar da dubban shahidai a lokacin yakin Gaza da ma sauran lokuta da haramtacciyar kasar Isra’ila take kaddamar da hare-haren ta’addanci a kansu, saboda haka sun kai ga matsaya kan cewa duk wata tattaunawa da yahudawan sahyuniya ba za ta taba baiwa palastinawa ‘yancinsu da kwato wurarensu ba sai ta hanyar gwagwarmaya da makami.
Yanzu haka dai palastinawa sun ataruka na tunawa da yakin haramtacciyar gwamnatin yahudawa kan al’ummar muuslmi na yankin Gaza, inda ta kashe mutane akalla 1400, akasarinsu kanan yara da mata, lamarin da ya fuskanci kakkausar suka da Allawadai daga kasashen duniya.
925492

captcha