IQNA

Jami’iyar Adawa Ta Ksar Bahrain Ta Yi Allawadai Da Keta Hurumin Masu Fafutuka

18:23 - January 08, 2012
Lambar Labari: 2253429
Bangaren kas ada kasa, babbar jam’iyar adawa a kasar Bahrain ta Al-wifaq ta yi kakkausar tare da yin Allawadai kan keta hurumi da cin zarafin masu fafuka a kasar da jami’an tsaron masarautar sarki Hamad ke yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wifaq cewa, babbar jam’iyar adawa a kasar Bahrain ta Al-wifaq ta yi kakkausar tare da yin Allawadai kan keta hurumi da cin zarafin masu fafutuka a kasar da jami’an tsaron masarautar sarki Hamad ke yi duk kuwa da gargadin da kun giyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa suka yi kan hakan.
A bangare guda kuma babban sakataren jam'iyyar adawa ta Ahrar da ke kasar Bahrain ya jaddada cewa: Gwamnatocin Amurka da Birtaniya suna da hannu a murkushe 'yan adawar kasar Bahrain.
Sa'id As-Shahabi ya bayyana cewa: Akwai manyan jami'an sojin Amurka da na Birtaniya da suke cikin kasar Bahrain a halin yanzu haka suna horas da jami'an tsaron Bahrain hanyar da za su bi wajen murkushe al'ummar kasar da suke boren neman hakkokinsu na siyasa da zamantakewa.
As-Shahabi ya kara da cewa; a farkon yunkurin al'umma a Bahrain jama'a suna neman a gudanar da gyare-gyare ne a harkar siyasar kasar, amma a halin yanzu barnar mahukuntan kasar ta sanya al'ummar Bahrain suna neman canjin gwamnati ne a kasar.
930281

captcha