Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Two Circles cewa, ana ci gaba da gudanar da wani taron baje kli na littafan addinin muslunci a Lakhano na kasar India wanda kungiyoyin musulmi da cibiyoyi suke shirya tare da halartar masana daga sassa na kasar ta India da suka hada musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Wani rahoton na daban kuma yana cewa, kasar China ta yi watsi da takunkumin bangare guda wanda kasar Amurka ta dorawa kasar Iran na baya bayan nan, mai magana da yawun gwamnatin kasar ta China Hong Lie ya fadawa taron yan jaridu a jiya laraba cewa, harkokin tattalin arziki tsakanin kasar China da Iran zasu ci gaba kamar yadda aka saba. Don hakan inji shi bai sabawa dokokin kasa da kasa ba.
Shugaban Baraka Obama na kasar Amurka ya sanya hannu a kan wata doka wacce ta bukaci ladabtar da duk wata cibiyar kudi ko kuma wata kasa da ta shiga hulda ta harkokin kudi ko kuma na man fetur da kasar Iran.
Dokar ta bawa manya manyan bankuna a kasashen duniya da su zabi hulda da kasar Amurka ko kuma Iran. Duk wata kasa da ta shiga harkar kudi ko ta sayi danyen man na kasar Iran to gwamnatin Amurka zata yanke hulda da su.
Dokar dai, ba zata fara aiki ba sai bayan watannin 6, don bawa kasashe da kuma cibiyon kudade a duniya wadanda suke hulda da Iran da su nemi sabbin abokan hulda kafin lokacin.
931192