Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami'ar Azhar ya yi kakakusar suka matakin da yahudawan sahyuniya suka dauka na cire dutsen sakhra a masallacin Qods a wani mataki na tsokanar al'ummar musulmi da sauran mabiya addinai da aka safkar daga sama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Almadian cewa, babban malamin jami'ar Azhar ya yi kakakusar suka matakin da yahudawan sahyuniya suka dauka na cire dutsen sakhra a masallacin Qods a wani mataki na tsokanar al'ummar musulmi da sauran mabiya addinai da aka safkar daga sama da suka hada muslunci da kiristanci.
A nasa bangaren babban sakataren jam'iyyar adawa ta Ahrar da ke kasar bahrain ya jaddada cewa: Gwamnatocin Amurka da Birtaniya suna da hannu a murkushe 'yan adawar kasar, Sa'id As-Shahabi ya bayyana cewa: Akwai manyan jami'an sojin Amurka da na Birtaniya da suke cikin kasar a halin yanzu haka suna horas da jami'an tsaron Bahrain hanyar da za su bi wajen murkushe al'ummar kasar da suke boren neman hakkokinsu na siyasa da zamantakewa.
As-Shahabi ya kara da cewa; a farkon yunkurin al'umma a kasar jama'a suna neman a gudanar da gyare-gyare ne a harkar siyasar kasar, amma a halin yanzu barnar mahukuntan kasar ta sanya al'ummar suna neman canjin gwamnati ne a kasar.
931049