Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Lofikaro cewa, babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi kakausar suka da yin Allawadai da ci gaba da gina matsugunnan yahudawa da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi a cikin yankunan palastinawa da ke gabacin birnin Qods.
Bangare guda kuma takunkumi sayarda danyen man fetur na bangare guda wanda kasar Amurka take son dorawa danyen man fetur na kasar Iran ba zai kai ga nasara ba, wannan shi ne labarin da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto gidan Television na Asia News a wani rahoton da ya gabatar a safiyar yau litinin.
Gidan television na Asia News daga kasar Malasia ya bayyana cewa, kasashen China da Rasha sun bayyana matsayinsu, kamar sauran kasashen yakin na cewa ba za su yi aiki da takunkumin da kasar Amurka ta dorawa danyen kasar Iran ba.
Asia News ya kara da cewa kasashen turai da dama suna tababar yin aiki da wannan takunkumin, don abinda zai jawo na kara tabarbarewar tattalin arzikin duniya.
936011