Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, limamin masallacin juma'a a birnin Beierut na kasar Lebanon ya gana da wasu daga cikin manyan malaman addinin kirista na kasar dangane da muhimmancin kara karfafa dangantaka tsakanin mabiya addinan biyu wadanda suke da yawa a kasar.
Babban kwamandan askarawan kasar Labanan Janar Jean Qahwaji, ya ce kasar za ta yi iya kokarinta domin hana ci gaba da fasakwabrin makamai daga kasar zuwa kasar Sirya wadanda 'yan ta'adda ke yin amfani da su wajen kai hare-hare a kasar.
A yau alhamis, janar Qahwaji ya bayyana cewa yanzu haka rundunar sojan kasar ta dauki matakan da suka dace domin kare iyakokin kasar ta Labanan da kuma hana masu aike wa da makami zuwa Syria daga kasar.
Babban hafsan sojojin kasar ta Labanan a dai ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar da aka yi tsakanin Jakadan Syria a Labanan da kuma Firayi ministan kasar ta Labanan Najib Mikati, inda kuma jami'an biyu suka tattauna wannan batu da kuma yadda za'a warware shi a tsakaninsu.
938377