Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na kamafanin diallncin labaran europe1 cewa, ma’aikatr kula da harkokin cikin gida na kasar Faransa ya sanar cewa za agudanar da wasu ‘yan canji a cikin kundin tsarin majalisar mabiya addinbin muslunci a kasar domin samun damar shiga cikin harkoki da dama na kasar a dama da su maimakon zama saniyar ware a cikin harkoki kasar.
A jiya ne aka gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Zainul Abidin Bin Ali.
Mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga kasar Tunisia ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan a hukumance a birnin Tunis, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a wasu biranan kasar, inda suka yi Allawadai da ziyarar sarki Qatar a kasarsu, wanda yake halartar bukukuwan cika shekara guda da samun juyi a kasar.
Dubban masu zanga-zanga a birnin Saqas na kasar Tunisa, sun daga kyallaye da kwallaye da aka rubuta cewa, sarki Qatar Karen farautar Amurka da yahudawa ne, saboda haka al'ummar Tunisia ba su lalae marhabin da shi a kasarsu.
941308