Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci ta hzibullah a kasar Lebanon sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa taimakon da Iran ta yi wa kungiyar shi ne bababn dalilin samun nasarar da ta yi a lokacin yakinta da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmayar musulunci ta hzibullah a kasar Lebanon sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa taimakon da Iran ta yi wa kungiyar shi ne bababn dalilin samun nasarar da ta yi a lokacin yakinta da haramtacciyar kasar Isra’ila a yakin da ta kaddamar a kan al’ummar kasar a cikin shekar ata dubu biyu da shida.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov da shugaban kungiyar leken asiri na kasar Mikhail Paradakov sun isa kasar Siriya don tattaunawa da shugaban kasar Bashar al-Asad, rahotanni daga kasar Siriyan sun bayyana cewar dubun dubatan al'ummar kasar Siriyan ne suka yi cincirindo a kan titunan da Mr. Lavrov din zai bi don yi maraba da shi da kuma bayyanar da godiyarsu da hawa kujeran nakin da kasar ta yi kan kudurin da kasashen yammaci da larabawa suka gabatar a kwamitin tsaro wanda al'ummar suke ganinsa a matsayin gagarumin makirci na nufin wargaza kasar.
A wani lokaci a nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Rashan zai gana da shugaba Asad don tattauna hanyoyin da za a bi wajen magance rikicin da ke ci gaba da faruwa a kasar Siriyan wanda kasashen yammaci da taimakon kawayensu na kasashen larabawa suke ci gaba da rura shi da nufin daukan fansa a kan gwamnatin Asad din da suke ganinta a matsayin kafar ungulu ga manufofinsu a wannan yankin.
949799