Bangaren kasa da kasa: a yau hasken farkawar musulmi ya haskakawa a yankuna daban daban da kuma ci gaba da yaduwa inda a halin yanzu ya fara haskawa da mamaye yankin asiya ta tsakiya duk da kokari da zagon kasan murkushe shi da gwamnatoci da mahukumtan yankin ke kokarin yi ta fuskar amfani da mahanga ta siyasa da dai sauran matakai makamantan hakan.