IQNA

An Girmama Iyalan Wadanda Suka Taka Rawa A Fagen Kur'ani A UAE

21:20 - February 18, 2012
Lambar Labari: 2276418
Bangaren kasa da kasa, an girmama iyalan mutanen da suka nuna kwazo ta fuskacin kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa da nufin kara karfafa gwiwarsu ta wannan fuska, ta yadda za su za su zama abin buga misali ga sauran Al'ummar kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-bayan cewa, an girmama iyalan mutanen da suka nuna kwazo ta fuskacin kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa da nufin kara karfafa gwiwarsu ta wannan fuska, ta yadda za su za su zama abin buga misali ga sauran Al'ummar kasar, wadanda akasaeinsu mabiya addinin muslunci ne.

A bangare guda kuma babban sakataren kiungiyar Hizbullah ta kasar labanan sayyin nhassan Nasrullah ya zargi AMurka da Haramtacciyar Kasar Israila da wasu kasashen Larabawa da kuma kungiyar Alkaida da kokarin kifarvda gwamnatin shugaba Bashshar Asad na kasar Siriya.
Sayy8id Nasrullah ya yi wannan bayani ne a jawabin da ya yi a dare jiya a birnin Beirut wanda aka watsa a talbijin a taron shekara ta hudu da shahadar shugaban bangaren tsaro na kungioyar Hizbullah wato Imad Mugniyah.

Nasrullah ya soki lamirin wasu kasashen Larabawa wadanda suke adawa da gwamantin Siriya yana maim cewa: "Idan muka bfada wa gwamnatocin kasashen Larabawa su yi tattauna da gwamnatin Siriya sai su ce lokaci ya riga ya kure, amma me ya sa su ka amince su tattauna da Israila amma ba zasu tattauna da Siriya ba wacce kasar ce ta Larabawa?" in ji Sayyid Nasrullah.

954884





captcha