IQNA

Zaman Taron Islam-abad Ya Jaddada Muhimmancin Iran A Yankin Baki Daya

15:18 - February 19, 2012
Lambar Labari: 2276905
Bangaren siyasa da zamantakewa, zaman taron da aka gudanar na hadin gwiwa tsakanin kasashen Iran da Pakistan da kuma Afghanistan a birnin Islamabad ya jaddada muhimamncin da Iran take da shia acikin dukaknin harkoki na yankin gabas ta tsakiya baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa zaman taron da aka gudanar na hadin gwiwa tsakanin kasashen Iran da Pakistan da kuma Afghanistan a birnin Islamabad ya jaddada muhimamncin da Iran take da shia a cikin dukaknin harkoki na yankin gabas ta tsakiya baki daya musamman ma a wannan lokaci da yankin ke fuskantar matsaloli na tsaro daga wajen yankin.
A wani labarin kuma ana shirin gudanar da wani taron hadin kan kasa a kasar Iraki da nufin samun fahimtar juna tsakanin dukaknin bangarorin siyasa a daidai lokacin da wasu kasashen larabawa suke kullawa kasar Iraki makirci da nufin kawo baraka tsakaninsu musamman ma ganin cewa kasar ba ta koma karkashin ikonsu ba bayan kawar da Saddam kamar yadda suka yi tsammani.
Malaman addinin muslunci a kasar Iraki sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai kan miliyoyin mutanen da suka gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a yankunan kasar Iraki domin kawo cikas ga wadannan taruka.
Miliyoyin mutane ne su ke ci gaba da juyayin zagayowar kwanaki 40 na ashura a birnin Karbala na kasar Iraki, rahotannin da su ke fitowa daga Karbala sun ce ana hasashen cewa mutanen da su ka cika birnin sun haura miliyan 10, da su ka hada mutanen kasar da kuma bakin da su ka zo daga kasashen makwabta.
Miliyoyin Irakawa ne dai su ka ti tattaki da kafafunsu daga garuruwa masu nisa domin zuwa karbala. 955196
captcha