Bangaren siyasa da zamantakewa: Ayatullahi Uzma kuma mai bincike mutuman Kabul kuma babban marji'I a duniyar musulmi a daidai lokacin da aka sanar das hi yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a Afganistan suka kona kur'ani mai tsarki ya bayyana cewa: cin mutunci da wulakanta kur'ani mai girma yana nufin cin mutunci da wulakanta sama da biliyan daya da rabi na musulmin a fadin duniya baki daya ne
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Ayatullahi Uzma kuma mai bincike mutuman Kabul kuma babban marji'I a duniyar musulmi a daidai lokacin da aka sanar das hi yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a Afganistan suka kona kur'ani mai tsarki ya bayyana cewa: cin mutunci da wulakanta kur'ani mai girma yana nufin cin mutunci da wulakanta sama da biliyan daya da rabi na musulmin a fadin duniya baki daya ne. Wannan babban ayatullahi kuma marji'I ya aike da sako da fara cewa bayan bismillahi rahamani rahimi duk wanda ba ruwansa da lamarin day a shafi musulmi baya cikin musulmi hadisi day a zo a cikin Kafi juzi'I na biyu shafi na dari da satin da uku don haka ya nuna damuwa dab akin cikinsa da jin labarin kona wasu kur'anai masu tsarki da wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka yi inda ya tsine masu albarka da yin Allah wadai da wannan mummunan aiki na sun a takalar fada da neman tada fitina da cewa wannan wani mataki ne na rashin kare hakkin dan adam .
960092