IQNA

Musulmin Kasar Faransa Sun Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Kur'ani A Kasar Afghanistan

22:57 - February 29, 2012
Lambar Labari: 2283499
Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Faransa ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a cikin makon day a gabata tare da kiran dakarun ammaya da su fice daga kasar musulmi.

Kamfanin dilalcnin cin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo tf1 cewa, majalisar musulmin kasar Faransa ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a cikin makon da ya gabata tare da kiran dakarun mamaya da su fice daga kasar musulmi da suke tozarta ma'abotanta.
A wani zama da suka gudanar a babban masallacin marsel wanda shi ne daya daga cikin muhimman wurare da musulmi suke gudanar da harkokinsu, sun cimma matasa kan bayanin da suka fitar da ke yin Allawadai da cin zarafin musulmi da keta alfarmar kur'ani mai tsarki a kasar Afghanistan, tare da kiransu das u fice su bar kasar cikin gaggawa.
Majalisar musulmin kasar Faransa ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a cikin makon day a gabata tare da kiran dakarun ammaya da su fice daga kasar.
961866

captcha