Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babban malimin addinin muslunci na jami'ar Azahar sheikh Ahmad Tayyib ya kirayi Amurka da ta gaggauta ficewa dag akasar Afghanistan domin kuwa acewarsa, abin da ta yin a ci zarafin kur'ani shelanta yaki ne kan alu'mmar musulmi na duniya baki daya.
A wani labarin kuma jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun sake rufe mashigar Karam Abu Salim da ke gabacin yanzkin zirin Gaza, a yunkurin baya-bayan na da kara takura palastinawa mazauna miliyan 1 da rabid a rayuwa ayankin.
A wani rahoto da shafin sadarwa na Al-risalah Net ya watsa a yau ya bayyana cewa, shugaban kwamitin kula da mashigar Karam Abu Salim Ra'id Fattuh ya sheda cewa, a yau jami'an tsaron yahudawan sahyuniya sun rufe wannan mashiga, inda suka hana shigar da kayan abinci da ayyuka a wannan yanki, wanda ya kwashe shekaru yahudawa na killace das hi.
A wani labarin kuma 'Yan sandan yahudawan Isra'ila sun kai farmaki a safiyar yau a yankunan palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kame palastinawa da dama suka ci zarafinsu, kuma suka yi awon gaba da su ba tare da wani dalili ba.
961897