Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu masana suna ganin cewa kone kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Afghanistan ya tabbatar das u wane ne suke bin sahihin tafarki na addinin msluci da kuma wadanda suke rayawa, domin kuwa shirin da kasashen musulmi suka yi ya tabbatar da cewa akwai munafukai masu daurewa kafirci gindi.
Jami'an tsaron kasar Bahrain da sojojin kasar Saudiyya ke marawa baya sun kai farmaki a yau a yankin Sahla da ke kudancin birnin Manama, inda suka kashe wani magidanci a cikin iyalinsa.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga kasar Bahrain ya bayyana cewa, jami'an tsaron kasar ta Bahrain sun sha alwashin daukar dukaknin matakai na rashin imani a kan duk wanda ya sake fitowa zanga-zangar neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar, wadda mutanen kasar suka kwashe sama da shekara guda suna gudanarwa domin neman hakkokinsu da aka haramta musu.
Rahoton ya kara da cewa, jami'an tsaron an Bahrain da sojin Saudiyya ke rufa musu baya da motoci masu sulke, sun kashe Habib kazim Al-mulla a cikin gidansa a yau, tare da yin awon gaba da wasu mutane da dama, bisa zarginsu da yin bore ga masautar kasar.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human rights Watch ta kirayi mahukuntan Bahrain da su daina cin zarafin dan adam, kuma su gaggauta sakin muatnen da suke tsare da su a gidajen kurkuku saboda ra'ayoyinsu na siyasa.
961932