IQNA

Malaman Addini A yankin Kurdistan Sun Yi Allawadai da Keta Alfarmar Kur’ani

20:28 - March 03, 2012
Lambar Labari: 2284712
Bangaren kasa da kasa, babbar kungiyar malaman addinin muslunci da ke yankin Kurdistan ta kasar Iraki sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da ke ta alfarmar kur’ani mia tsarki ta hanyar kone wasu shafukansa kamar yadda wani bayani da suka fitar ya yi nuni.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sautul Iraq cewa, kungiyar malaman addinin muslunci da ke yankin Kurdistan ta kasar Iraki sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da ke ta alfarmar kur’ani mia tsarki ta hanyar kone wasu shafukansa kamar yadda wani bayani da suka fitar ya yi nuni da hakan.
Bayanin malaman ya ci gab ada cewa, wajibi ne a dauki dukaknin matakan da suka dace domin ladabtar da duk wanda ya aiakata wani laifi na cin zarafin da keta alfar kur’ani mai tsarki, tare da bayyana kone shafukan kur’ani da wani mutum ya yi da cewa hakan ya yi hannun riga da koyarwar dukkanin addinai da ma dabi’a ta dan adam.
Bisa ga bayanin da aka watsa, wani mutum ya kone wasu shafika na kur’ani mai tsarki, da suka hada har da wasu ayoyi masu albarka daga cikin surat Anfal, bisa hujjar cewa suna dag acikin ayoyin da Saddam ya yi amfani da su wajen yin kisan kiyashi kan kurdawa a cikin shearun tamanin da wani abu, kuma ya dauki hoton abin da ya yi ya saka a shafin yanar gizo na facebok domin kowa ya gani.
963754

captcha