IQNA

Rawar Da Gwagwarmayar Ta taka Wajen Gyara Ma Amurka Da Yahudawa Zama

20:17 - March 07, 2012
Lambar Labari: 2287698
Bangaren kasa da kasa, abubuwan da suka faru a kasar Syria da kuma yadda muatanen kasar suka fito da bababn rinjaye wajen kada kuriunsu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar hakan ya tabbatar da cewa yin tsayin daka da gwamnatinSyria ta yi a kan abubuwan da ta yi imani da su shi ne babban sirrin nasarata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin masana masu sharhi kan harkokin yankin gabas ta tsakiya Ahmad Kazim Zadeh ya bayyana cewa, abubuwan da suka faru a kasar Syria da kuma yadda muatanen kasar suka fito da bababn rinjaye wajen kada kuriunsu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar hakan ya tabbatar da cewa yin tsayin daka da gwamnatinSyria ta yi a kan abubuwan da ta yi imani da su shi ne babban sirrin nasarata a kan makiya, da suka hada da Amurka da ‘yan amshin shatanta turawa da kuma yar lelenta haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya, gami da karnukan farautarta na daga kasashen yankin.
Ya ci gaba da cewa musallacin gawagwarmaya, wanda ya hada Iran, Syria, Hizbullah a lebanon, ya tabbatar da cewa babu canji a cikin matsayinsa akan dukaknin lamurra da suka danganci wannan al’umma, kuma yunkurin makiya ba zai iya dakushe wannan hankoro na masu kokarin tabbatar da adalci a cikin al’umma ba.
Dangane da batun Bahrain kuma, ya jadda cewa mahukuntan kasar suna zaton cewa ta hanyar yin amfani da karfi ne za su iya murkushe fararen hula masu zanga-zangar neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar ta hanyar lumana, amma dag abisani ta bayyana cewa sun tafka babban kure, domin kuwa mutane suna bukatar ‘yancinsu ne da kuma hakkokinsu da aka haramta musu.
965203

captcha