IQNA

Shugaban Kasar Tunusiya Ya Bukaci Hukumta Masu Kafirta Wasu

15:27 - March 08, 2012
Lambar Labari: 2287944
Bangaren kasa da kasa: Munsaf Almarzuki shugaban kasar Tunusiya ya bukaci masu yin dokoki a kasar da su samar da wata doka za ta hukumta duk wani da aka samu yana kafirta wani musulmi.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Munsaf Almarzuki shugaban kasar Tunusiya ya bukaci masu yin dokoki a kasar da su samar da wata doka za ta hukumta duk wani da aka samu yana kafirta wani musulmi.Shuagaba na Tunusiya ya ci gaba da jaddada cewa; masu fitar da fatawar kafirta wasu daga cikin musulmi ko kafirta wasui malamai yana yi wa hadin kasa da zamantakewar kasar Barazana saboda haka ya yi kira ga komitin da ke samar da doka a kasar ta Tunusiya day a samar da wata doka da za ta hukumta duk wanda aka sami da fitar da fatawar kafirta wani a kasar ko kuma ya kafirta wasu daga cikin mabiya wata daga cikin mazhabobin musulunci a fadin kasar.Har ila yau ya kara da cewa irin wanna fatawa ta yi hannun rika da duk wani tunani da nazari kuma wani kokari ne na haddasa fitina da Baraka a tsakanin yan kasar ta Tunusiya musulmi musamman da suke neman a kara hadin aki a tsakanin musulmi ba tare da yin la'akari da mazhabarsa ba.
967104

captcha