IQNA

Kasashen Turai Na Gasar Samun Matsayi Ta Hanyar Yada Kyamar Musulunci

20:19 - March 11, 2012
Lambar Labari: 2289859
Bangaren kasa da kasa, abubuwan da suka faru na cin zarafin musulmi da addinin muslunci a kasashen turai daban-daban, wata alama ce da ke nuni da cewa al’ummomin wadanan kasashen da ‘yan siyasarsu da shugabanninsu suna yin amfani da nuna adawa da musulunci da kuma yada kyamarsa atsakanin mutane a matsayin wata hanya ta neman matsayi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, da dama daga cikin masana musulmi sun imanin cewa abubuwan da suka faru na cin zarafin musulmi da addinin muslunci a kasashen turai, da hakan ya hada da yada hotuna na zanen batunci ga manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, wata alama ce da ke nuni da cewa al’ummomin wadanan kasashen da ‘yan siyasarsu da shugabanninsu suna yin amfani da nuna adawa da musulunci da kuma yada kyamarsa atsakanin mutane a matsayin wata hanya ta neman matsayi na siyasa ko zamantakewa a cikin kasashen da suke gaba da musulmi da musulunci.
Har ila daga cikin irin wadannan munanan ayyukan da irin wadannan mutane suke aiwatarwa a kasashen yammacin turai har da sanar da ranar kone kur’ani ta duniya da wani la’antacen mutum ya yi a kasar Amurka ba tare da an ce masa uffan ba, da kuma zanga-zangar da wasu mutane suka yi akasar Jamus ta gaba da musulunci, daga karshe-karshen nan kuma sojojin Amurka sun banka wuta kan kur’ani mai tsarki a kasar Afghanistan.
Manufar hakan baki daya ita ce tsokanar musulmi, domin kuwa wanda zai yi haka ya san matsayin manzon allah da kur’ani a wajen musulmi, taba su ko keta alfarmarsu tamkar shelanta yaki ne kan addinin musulunci.
968533








captcha