Bangaren kasa da kasa: a wani taro da malamai musulmi na kasar Labanon suka gudanar a ranar ashirin da biyu ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun fitar da wata sanarwa da suke jaddada cewa; yin shuru da gum da baki kan hare haren ta'addanci da wuce gonad a irin a zaluncin da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta saba yi kan al'ummar Palasdinu da kuma wanda ta kai a baya bayan nan cin amana ne.
Kamfanin dillancin labarai na iKna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a wani taro da malamai musulmi na kasar Labanon suka gudanar a ranar ashirin da biyu ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun fitar da wata sanarwa da suke jaddada cewa; yin shuru da gum da baki kan hare haren ta'addanci da wuce gonad a irin a zaluncin da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta saba yi kan al'ummar Palasdinu da kuma wanda ta kai a baya bayan nan cin amana ne.An nakalto daga majiyart labarai ta gidan talbijin din Almanar ta kasar Labanon da ke watsa shirye-shiryenta ta hanayr tauraron dan adam cewa; a wanna taron da malaman addini na kasar ta labanon suka gudanar sun bayyana cewa: take hakkin dan adam da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi ya kai bai dace ba a yi shuru a kai ba kuma yin shiru da gum da baki ba a cewa komi kan ta'addancin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila da hare haren da ta ke kai wa al'ummar yankin zirin Gaza tamkar cin amana ne . taron malaman ya jaddada cewa: wadannan hare-hare da zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya zone a daidai lokacin da Ehud Barak ministan yaki na gwamnatin Haramtacciyar kasar isra'ila ya kuduri niyar shan jinin fararen hulan Palasdinu a wani yunkuri nasa na nuna karfi da rowan wuta kan al'ummar yankin zirin gaza kuma wannan a daidai lokacin da hukumomi da kasahen duniya da kungiyoyi na kasa da kasa da na yankin suka yi gum da bakinsu bas u cewa komi kan wannan mummunan aiki.
971012