IQNA

Al’ummar Kasar Tunisia Sun Gudanar Da Gangami Na Kare Martabar kur’ani

20:05 - March 25, 2012
Lambar Labari: 2294601
Bangaren kasa da kasa, al’ummar kasar Tunisia sun gudanar da wani gagarumin gangami domin kare martabar kur’ani mai tsarki a birnin Tunis fadar mulkin kasar tare da halartar dubban mutane daga bangarori daban-daban na al’ummar kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mutanen kasar Tunisia sun gudanar da wani gagarumin gangami domin kare martabar kur’ani mai tsarki a birnin Tunis fadar mulkin kasar tare da halartar dubban mutane daga bangarori daban-daban na al’ummar kasar wadda keda mutane sama da miliyan sha daya, kuma akasarinsu musulmi.
A nata bangaren ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Tunisia ce ta sanar da hakan, wanda kuma zai ci gab aa kowace shekara, kasantuwar canjin da aka samu a kasar ba zai bayar da damar ci gaba da cin zarafin addinin muslunci kamar gwamnatin da ta gabata ba, wadda ta shara da kare manufofin kasashen yammacin turai da kuma aiwatar da su kan mutanenta.
Ranar juma’ar da ta gabata a sanar da ita a matsayin ranar kasa ta kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia domin mayar da martani kan cin zarafi da keta alfarmar kur’ani da wani dan kasar ya yi a kawanakin baya da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda kuma hakan wani gagarumin ci gaba da al’ummar kasar ta samu sakamakon juyin juya halin da ta yi.
974732
captcha