Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkokin bil adama takasar Bahrain ta gudanar da wani taron baje koli na ta’asar da masautan kasar Bahrain suke tafakawa kan fararen hular masu neman sauyi na siyasa da harkokin mulki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na qawem.org cewa, kungiyar kare hakkokin bil adama takasar Bahrain ta gudanar da wani taron baje koli na ta’asar da masautan kasar Bahrain suke tafakawa kan fararen hular masu neman sauyi na siyasa da harkokin mulki na kasar baki daya.
A yayin gudanar da taron baje kolin masana da mamalan addini da kuma lauyoyi gami da masu rajin kare hakkin bil adama na kasar Bahrain da Lebanon da wasu kasashe sun halarci wannan baje koli da aka shirya a birnin na Beirut, domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Bahrain da ake zalunta mafi sharrin zalunci.
Kungiyar kare hakkokin bil adama takasar Bahrain da ta gudanar da taron na baje koli na ta’asar da masautan kasar Bahrain suke tafakawa kan fararen hular masu neman sauyi na siyasa da harkokin mulki a kasar, ta jaddada wajabcin ci gaba da goyon bayan fararen hular na Bahrain, tare kamanta gaskiya daga kasashen larabawa da suka yi watsi da hakan.
975892