IQNA

Za A Gudanar Da Wani Baje Koli Na Kayayyakin Abin Halal A Kasar Faransa

16:11 - April 02, 2012
Lambar Labari: 2296623
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani baje koli na kayan abinci na halal a birnin paris na kasar faransa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin mabiya addinin muslunci wadanda suke da dangantaka da kamfanonin kasar da suke samar da ababen bukata bisa yarjejeniya a tsakaninsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo sepher news cewa, ana shirin gudanar da wani baje koli na kayan abinci na halal a birnin paris na kasar faransa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin mabiya addinin muslunci wadanda suke da dangantaka da kamfanonin kasar da suke samar da ababen bukata bisa yarjejeniya a tsakaninsu da wadannankamfanoni, inda a halin yanzu za su kawo kaya na ahalal bisa yarjejeniyar.
Baje kolin zai nuna irin kayan da ake samarwa a kasashen muslmi da suke samar da kayan abincin halal kuma suke fitar da su zuwa kasashen ketare, daga ciki kuwa har da kamfanonin kasashen malazia da Indonesia gami da wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa, baje kolin zai taimaka matuka wajen banbance kayayyakin a tsakanin sauran kayan abinci da ake sayarwa a shaguda da kwasunnin kasar.
Gudanar da wannan baje koli na kayan abinci na halal a birnin paris na kasar faransa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin mabiya addinin muslunci wadanda suke da dangantaka da kamfanonin kasar da suke samar da ababen bukata bisa yarjejeniya a tsakaninsu yana da matukar muhimmanci ga mabiya addinin muslunci da suke zaune a kasar wadda ba ta musulmi ba.
977103


captcha