Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine cewa, muhammad Uraifi malamin wahabiyawan Saudiyya da ya ci zarafin manzon Allah tsira da maincin Allah su tabbata agare shi ya fito ya nemi uzurin dukkanin muslumi a lokacin da ya ga babu sarki sai Allah bayan da musulmin duniya baki daya suka yi ca a kansa, inda ya bayyana cewa ya amince da tafka kure kan abin da ya furta kan ma’aiki da sahabbansa.
Muhammad Uraifi wanda daya ne daga cikin fitattun malaman wahabiyawan Saudiyya ya bayyana cewa, gjiya ba najasa ba ce kuma ya halasta ayi salla da iya koda ta taba kayan mutum ko jikinsa, saboda wasu dalilai da ya kawo daga cikin akidarsa ta wahabiyanci, da ke cewa wai manzon Allah ya kasance yana samun kyuatar giya daga sahabbai kafin a haramtata, kuma ana zubar da giiya alokacin sahabbai suke masallaci suna takawa kuma su je su yi sallah, ba tare da manzon Allah ya ce sun taka najasa ba.
Malamin wahabiyawan na Saudiyya da ya ci zarafin manzon Allah tsira da maincin Allah su tabbata agare shi ya fito ya nemi uzurin ne daga dukkanin muslumi a lokacin da ya fhinci cewa rayuwarsa na cikin hadari, amma babu wani tabbaci kan cewa uzurin da ya nema yan anufin ya dawo dag akan ra’ayinsa na keta alfarmar addinin muslunci.
977476