IQNA

Masu Taron Birnin Damascus Sun Bukaci Taka Ma Isra’ila Birki Kan Yahudantar Da Qods

12:46 - April 14, 2012
Lambar Labari: 2303404
Bangaren kasa da kasa, daruruwan malaman addinin musluci ne suka halarci taron hadakar malaman Sham a birnin Damascus na kasar Syria inda suka yi kira da atakawa haramtacciyar kasar Isra’ila birki kan hankoron da take na yahudantar birnin Qods mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na SANA cewa, daruruwan malaman addinin musluci ne suka halarci taron hadakar malaman Sham a birnin Damascus na kasar Syria inda suka yi kira da atakawa haramtacciyar kasar Isra’ila birki kan hankoron da take na yahudantar birnin Qods mai alfarma musamman ma take-takensu na cikin ‘yan lokutanan.
Gwamnatocin kasashen Rasha da China sun kirayi 'yan tawayen Syria da su dakatar da bude wuta ba tare da wani bata lokaci ba, bayan da dakarun gwamnati suka janye da dukkanin yankunan da ake fama da rikici a kasar.
A cikin bayanan da suka fitar ma'aikatun harkokin waje na kasashen Rasha da China, sun jaddada cewa wajibi ne kan 'yan tawayen Syria su dakatar da bude wuta, domin kuwa gwamnatin Syria ta yi aiki da yarjejeniyar da ta cimmawa tare da mai shiga tsakani a rikicin na Syria Kofi Annan.
A nata bangaren gwamnatin kasar Birtaniya, wadda kuma tuni gwamnatin Syria ta bayyana ta a matsayin daya daga cikin bangarorin rikicin, ta bayanna cewa za ta kara runbaya taimakon da take baiwa 'yan tawayen na Syria domin su ci gaba da abin da suke yi.
Yayin da ministan tsaron kasar Saudiyya ya nufi kasar Amurka, domin ganawa da sakataren tsaron Amurka kan hanyoyin da za su bi wajen ci gaba da taimaka ma 'yan bindiga a kasar Syria, duk kuwa da dakatar da bude wuta daga bangaren dakarun gwamnati.
983768
captcha