Bangaren kasa da kasa, babban kwamitin mabiya addinin mulsunci a kasar Filland ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da kai harin ta’addancin da wasu suka yi kan wakilin manyan malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar Iraki.
Kamfanin dilalncin labaran iqn ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sautul iraq cewa, babban kwamitin mabiya addinin mulsunci a kasar Filland ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da kai harin ta’addancin da wasu suka yi kan wakilin manyan malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar Iraki tare da bayyana hakan da cewa wani yunkuri ne na masu hankoron haddasa fitina acikin muslumi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kai wani hari malamin addinin muslunci a kasar Iraki ba da nufin yin kisan gilla akansa, amma hakan bai hana al’ummar kasar ci gaba da bin sahihin tafarkin iyalan gidan amnzo ba, tare da kiran da malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzo suke yi na ci gaba da yin hakuri kan wadanna ayyuka.
Babban kwamitin mabiya addinin mulsunci a kasar Filland ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da kai harin ta’addancin da wasu suka yi kan wakilin manyan malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar Iraki a cikin makonnan, amma Allah ya kare shi.
983711