Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Beirut na kasar Lebanon, wanda ya mayar da hankali kan irin gagagrumar gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar wajen hada kan al’ummar musulmi wanda kuma hakan ya zama babban abin buga misali da shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Beirut na kasar Lebanon, wanda ya mayar da hankali kan irin gagagrumar gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar wajen hada kan al’ummar musulmi wanda kuma hakan ya zama babban abin buga misali da shi a cikin rayuwarsa.
A nata bangaren hukumar wucin gadin kasar Libya ta sanar da cewa ta sami bayanai kan batun Sayyid Musa Sadr jagoran addini a kasar labanan wanda ya bace a kasar Libya shekarar 1978 bayan gayyatar da tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi ya yi, shugaban hukumar wucin gadin ta Libya Mustafa Abduljalil ya sheda wa tashar talbijin ta France 24 cewa bayanai da suka samu suna nuni da an binse gawar Musa Sadr ne tare da wasu gawawwaki a cikin wani babban kabari a birnin Tarabulus fadar gwamnatin kasar.
Abduljalil ya kara da cewa ba za a bude kabarin ba sai a gaban idanun tawagar gwamnatin kasar Labanan, kuma daga bisani za a gudanar da binciken akan gwawwakin, amma wasu rahotanni sun habarta cewa miniustan harkokin wajen kasar Labanan Adnan Mansour ya bayyana rshin njin dadinsa kan yanda Abduljalil ya fitar da bayanai dangane da Musa Sadr saboda a cewarsa Labanan da Libya sun daidaita cewa ba zasu bayyana komai a kai ba sai bayan an gudanar da bincike.
983868