Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: rahotonni da ke fitowa a hukumce a kasar Ostriya na nuni da karuwar masu karbar addinin musulunci kuma yawancinsu suna barin addinin kiristanci ne zuwa addinin musulunci da hakan ke nuni da yadda addinin musulunci ke kara samin karbuwa a nahiyar Turai. Kasar Ostriya mai yawan al'umma miliyon takwas da yawancinsu al'ummar kasar Kiristoci mabiya darikar Katolika da kuma ked a dadden tarihi na shiga da karbuwar addinin kirsitanci a wannan kasar a yau lamari da yanayin kasar ya fara samin canji da sabon salo inda ake samin karbuwa da karuwar wadanda ke shiga addinin musulunci musamman kiristoci da ke canja sheka daga addinin kirsitonaci zuwa addinin musulunci kuma hatta al'adu da dabi'ar al'ummar kasar ta fara canjawa.
984908